Search
Close this search box.

Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane 40 A Yankin Karari Da Ke Omdurman Na Sudan

Mayakan dakarun kai daukin gaggawa na Sudan sun kashe mutane da dama a yankin Karari da ke birnin Omdurman na kasar Rahotonni sun bayanna cewa:

Mayakan dakarun kai daukin gaggawa na Sudan sun kashe mutane da dama a yankin Karari da ke birnin Omdurman na kasar

Rahotonni sun bayanna cewa: Jirgin saman yakin dakarun kai daukin gaggawa na rapid support forces ya yi luguden wuta kan yankin Karari da ke arewacin birnin Omdurman na kasar Sudan da ya yi sanadiyyar mutuwan mutane akalla 40 tare da jikkatan wasu fiye da 50 na daban.

Kwamitin shiga tsakani a rikicin kasar Sudan ya sanar da cewa: Akasarin wadanda suka mutun an kai su asibitin koyarwa na Al-Naw, sauran kuma zuwa asibitoci masu zaman kansu, yayin da sauran wadanda suka mutun aka binne su ba tare da an kai su asibiti ba.

Harin dai na zuwa ne kasa da sa’o’i ashirin da hudu bayan kisan kiyashin da aka yi a kauyen Wad Al-Nour na jihar Al-jazeera, wanda ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta zargi dakarun kai daukin gaggawa na rapid support forces da aikatawa, da kuma cin zarafin wadanda suke tsere da su a birnin El-Fasher fadar mulkin Darfur ta Arewa.

Wannan kisan kiyashi na Wad Al-Nour ya lashe rayukan fararen hula akalla dari da tamanin da suka hada da mata da kananan yara, don haka sojojin kasar Sudan sun lashi takwabin mayar da martani mai tsauri, tare da kin gudanar da zaman tattaunawa da wadanda ta bayyana a matsayin masu magoya bayan kungiyar Rapid Support forces ‘yan tawaye a Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments