Sojojin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Farmaki Kan Birnin Khalil Na Falasdinu

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan yankunan kudancin birnin Khalil a shirye-shiryen ba da dama ga tsagerun yahudawan sahayoniyya na mamaye wuraren kayan tarihi da suke birnin Rahotonni sun bayyana cewa: A yau Juma’a sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan wasu yankuna da dama da suke kudancin birnin Khalil […]

Ana Kiraye-kirayen Yin Zanga-zanga Gabanin Jawabin Netanyahu A Majalisar Dokokin Amurka

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin yin wani jawabi a majalisar dokokin Amurka a watan Yuli, matakin da ke janyo kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga a fadin Amurka. Shugabannin majalisar sun sanar da ranar 24 ga watan Yuli a matsayin ranar da zai gabatar da jawabi. A cikin wasikar da suka rubuta wa Netanyahu, Kakakin Majalisar […]

Guteres Ya Yi Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantar  MDD A Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da mummunan yakin Isra’ila a Gaza, yana mai tir da “sabon misali mai ban tsoro na ukubar da fararen hula suke sha”, a zirin a cewar kakakinsa. “Wannan wani misali ne mai ban tsoro na ukubar da Falasdinawa fararen hula, maza, mata da yara […]

‘Yan gwagwarmaya a Yaman da Iraki sun kaddamar da farmakin hadin gwiwa kan Isra’ila

Dakarun kasar Yemen da dakarun gwagwarmaya na kasar Iraki sun kaddamar da sabbin hare-hare na hadin gwiwa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, domin mayar da martani  kan yakin kisan kare dangi da take kan Falasdinawa a Gaza. Kakakin Rundunar Sojin kasar Yaman Brigadier General Yahya Saree ya fada a jiya Alhamis cewa, dakarun hadin gwiwa […]

Putin: Iran ta cika alkawuran da ta dauka kan yarjejeniyar nukiliya

A gefen taron na St.Petersburg, Putin ya kare matakin Iran na yin riko da alkawurra na yarjeneiyar nukiliya karkashin hukumar ta IAEA, yana mai nuni da yadda kasashen Rasha da Iran ke ci gaba da habaka hadin gwiwa a tsakaninsu a wani mataki na mayar da martani ga zagon kasar da kasashen yammacin duniya ke […]

Isra’ila Ta Sake Kashe Wani Adadi Na Mata Da Kanan Yara A Yankin Nusairat Da Ke Gaza

Rahotannin daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa, jiragen yakin Isra’ila suna ci gaba da kaddamar da munan hare-harea  dukkanin sassa na yankin babu kakkautawa. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Isra’ila ta kai hari kan ɗaya daga cikin makarantunta a Gaza “ba tare da yin gargaɗi ga dubban masu fararenn hula da […]