Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun nuna yadda suka halaka sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da raunata wasu tare da kama wasu a matsayin fursunonin yaki
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: Dakarunsu sun yi nasarar ritsawa da sojojin yahudawan sahayoniya a daya daga cikin ramukan karkashin kasa da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin Gaza, inda suka yi arangama da sojojin yahudawan sahayoniyya tare da halaka wasu daga cikinsu da raunata wasu na daban sannan suka kama wasu a matsayin fursunonin yaki.
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, faifan bidiyon ya fito ne daga Abu Ubaida, kakakin dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, wanda aka watsa a gidan talabijin na Aljazeera.