Rahotanni da suke fitowa daga Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ce, makamai masu linzamin da Iran ta harba sun sauka a yankunan Tel Aviv, Beit Shemish, da kuma Usdud.
Bugu da kari, Iran din ta kai wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na “Itmar” da aka gina a yammacin kogin Jordan hari, da ya haddasa tashin gobara. Haka nan kuma hare-haren na Iran sun isa zuwa Demona dake Naqab, sai kuma Bi’iru Sabaa.
Tashar talabijin din Aljazira ta ce, wasu gine-gine uku a matsugunin ‘yangsare wuri zauna na “Itamar” sun illata saboda faduwar makamai masu linzamin a kansu.
Miliyoyin ‘yan sahayoniya ne su ka gudu domin buya a karkashin kasa saboda hare-haren daga Iran.
A wani labarin na daban, kafafen watsa labarun Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ce, an kai wani harin da makami mai linzami daga kasar Yemen.