An cika kwanaki 216 da fara kisan kiyashi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi a Zirin Gaza na Falasdinu
Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifukan kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 216 a jere, ta hanyar kai hare-hare da dama ta sama da kasa da kuma harba makaman masu linzami kan yankunan Falasdinawa, lamarin da ke kai ga aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai a sakamakon hare-haren.
Rahotonni sun habarta cewa: Jiragen saman sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da kai kazaman hare-hare da muggan bama-bamai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza, baya ga ci gaba da kai hare-hare kan birnin Rafah ta kasa, inda suke ruguza gidaje, sansanonin ‘yan gudun hijira, tarwatsa tarurrukan jama’a da luguden wuta kan tituna, lamarin da ke janyo shahadan mutane da jikkatansu.