Azhar Ta Nemi A Samar Da Masu Shiga Tsakani A Rikicin Yankin

Cibiyar ta Azhar ta yi kira da a kafa kwamiti na ma'abota hikima a cikin wannan yankin domin kawo karshen yake-yake da sabani da suke
shugaban cibiyar Azhar

Cibiyar ta Azhar ta yi kira da a kafa kwamiti na ma’abota hikima a cikin wannan yankin domin kawo karshen yake-yake da sabani da suke faruwa da kuma karato da fahimtar juna.

A jiya Lahadi ne dai cibiyar ta Azhar ta yi wannan kiran na bukatar ganin an kafa kwamatin shiga tsakanin.

Shugaban cibiyar Azhar Sheikh Tayyib ya yi kira ga “Yan’uwa a cikin kasashen larabawa da kasashen musulmi” da su Fifita amfani da ruhin ‘yan’uwantaka da alaka ta addini da jini, da kuma aiki da hikima da ruhi na tattaunawa.”

Sheikh Ahmad Tayyib ya ce kwamitin da za a kafa zai yi aiki domin kawo karshen sabani a tsakanin Mabiya addini daya,kuma ‘ya’yan al’umma guda,domin kare karfin da suke da shi da kare rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.

Kiran na shugaban cibiyar Azhar ya biyo bayan sanarwar da ta fito daga bakin shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-sisi ne na cewa kasarsa za ta bayar da taimakon soja ga Saudiyya da take yaki da kasar Yemen.

Matsayin na kasar Masar dai ya Sanya Alamar tambaya akan rashin nuna damuwa irin wannan a lokacin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Gaza masu makwabtaka da ita kisan kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted