Araghchi: Macron Ba Zai Kubuta Daga Tallafawa Yaki A Iran Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi y ace shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ba zai kubuce daga laifin goyon bayan Amurka kan yakin da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi y ace shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ba zai kubuce daga laifin goyon bayan Amurka kan yakin da yta farwa kasar Iran da shi ba, wannan duk tare da mummunan halin da kasarsa take ciki na rike-rikicen mutanen kasar ba.

Tashar talabijan na Presstv a Tehran ya nakalto Aragchi yan fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, shugaban ya bayyana a baya kan cewa yana goyon bayan yakin da shugaba Trump ya fadawa kasar Iran da shi ba tare da wani dalili ba.

Ministan yace mutanen kasar Faransa bayan tsadar rayuwa da suke ciki, suna son a basu damar yencin taruwa don bayyana ra’ayinsu a kan al-amura da suka shafi rayuwarsu.

Daga karshe ya bukaci shugaban Faransa ya biya bukatun mutanen kasar Faransa, bay a farmasu da jami’an tsaro ba. Ya kula da bukatunsu bay a basu amsa da hayaki mai sa hawaye ko ya kama dukkan mutane har da masu kananann shekaru ya tsare su ba.

A cikin sakonsa na X Argchi ya aika wa Macron sakonsa ga trump a dai dai lokacinda yake nuna goyon bayansa ga Washington a cikin watan Jeneru kan matakan da yake dauka a kan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted