Sergei Lavrov Ya Fara Ziyarar Aiki A Tehran

Sergey Lavrov ministan harkokin wajen kasar Rasha ya isa birnin Tehran a yau litinin don ziyarar aiki. Kamfain dillancin labaran Isna na JMI ya bayyana

Sergey Lavrov ministan harkokin wajen kasar Rasha ya isa birnin Tehran a yau litinin don ziyarar aiki.

Kamfain dillancin labaran Isna na JMI ya bayyana cewa ziyarar  ministan ya zo ne karkashin ziyarar da suka saba yi na bin duddugin yarjeniyoyin da suka cimma a tsakaninsu a bayan da kuma ganin inda aka kwana a wajen aiwatar da su.

Hakama bangarorin biyu zasu tattauna halin da ake ciki a yankin da kuma al-amura da suka shafi kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted