Shugaban kasar Emanuel Macron, ya fara wani rangadi a yankin Gulf a daidai lokacin da kasarsa ke fama da rikici mai nasaba da boren tsadar rayuwa.
Macron dai ya sha suka sosai a karshen mako jiya bayan tashin hankalin da kasarsa ta tsunduma sakamakon boren jama’a.
A cikin jawabinsa a ranar Lahadi, Macron ya danganta matsalar Faransa game da tsadar rayuwa da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.
A cikin wannan yanayi ne shugaban Faransa ya tafi ziyarar ta kwanaki uku zuwa yankin Gulf, inda yake ziyarar kasashen : Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, da kuma Qatar.
Kafin nan dai Macron ya ki amincewa da murabus din ministan cikin gida na kasarsa a sakamakon suka da aka yi kan yadda aka tunkari masu zanga-zangar.
Rikicin ya yi sanadiyyar raunata kusan jami’an tsaro 1,000, sannan an kama mutane kusan 2,400, a cewar alkaluman hukuma.
Zanga-zangar da aka gudanar a duk fadin kasar ta hada dalibai da ke neman inganta yanayin ilimi da kuma jama’a da ke zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma durkushewar ayyukan gwamnati.
Mutane sama da rabin miliyan ne suka shiga zanga-zangar a ranar Asabar.
An wawashe gine gine, an yi ta kone-kone da lalata dukiya a birane da dama, inda masu zanga-zanga suka kai hari kan dakunan taro, ofisoshin ‘yan sanda da sauran gine-ginen gwamnati.
Zanga-zangar karshen mako mai cike da tashin hankali ta biyo bayan zanga-zangar makonni da daliban makarantar sakandare suka yi kan cunkoso a azuzuwa, karancin malamai da kuma rashin zuba jari a fannin ilimi.
Ana da fargabar zanga zanga ta yadu zuwa wasu kasashen turai, bayan ta bazu zuwa Belgium, Italiya da kuma spain.