Hukumar WFP Ta Rage Tallafin Jin Kai A Gaza

Hakan ya rage adadin mutanen da take taimakawa kowane wata da 500,000, yayin da take kira ga duniya da kada ta "juya baya ga yankin

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya (WFP) ta sanar da cewa dole ne ya tilasta mata rage ayyukan jin kai da take yi a Gaza saboda karancin albarkatu.

Hakan ya rage adadin mutanen da take taimakawa kowane wata da 500,000, yayin da take kira ga duniya da kada ta “juya baya ga yankin da yaki ya daidaita.

Tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hari a yankin Gaza, wanda aka kaddamar a matsayin martani ga harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, “iyalai da dama suka fada cikin matsanancin rayuwa na jin kai,”

Hakan dai na zuwa ne duk da tsagaita wuta da ya fara aiki shekara guda da ta gabata, kamar yadda Darektan Hukumar ta WFP, Shaun Hughes, a yankunan Falasdinawa ya shaidawa AFP.

Kimanin mutane miliyan 1.4, daga cikin mutane miliyan 2.1, “suna cikin mawuyacin hali na rashin abinci kuma suna bukatar taimakon jin kai don tsira.

A watan Agusta na shekarar 2025, Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana yunwa a Gaza, ikirarin da Isra’ila ta yi watsi da shi tana mai bayyana shi a matsayin “karya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted