Iran : Hadin Gwiwa Da Rasha Zai Inganta Zaman Lafiya A Yankin

An sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakanin ministan harkokin wajen Rasha dake ziyara a Tehran.

Iran ta ce hadin gwiwa da kasar Rasha zai karfafa zaman lafiya a yankin.

Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov dake ziyara a Tehran.

Mista Araghchi Ya ce hadin gwiwa da Rasha zai iya taimakawa wajen inganta zaman lafiya a yankin, yayin da kasashen biyu suka sake jaddada alkawarinsu na ci gaba da hulda kan batutuwan yanki da na duniya.

“Hadin gwiwa tsakanin Iran da Rasha zai taka rawa mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin. Mun ƙuduri aniyar ci gaba da dangantakarmu.”

Ya ce bangarorin biyu suna da ra’ayin cewa batutuwan yanki ba su da mafita ta soja kuma ya kamata a warware su ta hanyar diflomasiyya da hanyoyin siyasa.

Ya kara da cewa rashin tsaro a Tekun Farisa da Mashigin Hormuz sakamako ne “kai tsaye” na harin da sojojin Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Dangane da rikicin da ke tsakanin Afghanistan da Pakistan, Araghchi ya ce Iran da Rasha na da ra’ayoyi iri daya kan bukatar rage tashin hankali tsakanin Kabul da Islamabad.

Araghchi ya ce tattaunawar ta kuma shafi Falasdinu, Lebanon da Yemen, yana mai jaddada cewa dole ne a dakatar da kisan gillar da ake yi a Falasdinu.

Ministan harkokin wajen Rasha, a nasa bangaren, ya ce kasarsa ta na cika wajibcin da ke kanta a karƙashin yarjejeniyar hadin gwiwa ta dabarun yaki da Iran.

Ya jaddada cewa kasashen biyu sun kuduri aniyar ci gaba da fadada hadin gwiwarsu ta hanyar da ta dace da karfi duk da ci gaban yankin da matsin lamba daga waje.

Ministan harkokin wajen Rasha, wanda ke jagorantar wata tawagar diflomasiyya, ya isa Tehran ranar Litinin don ganawa da manyan jami’an Iran a ziyararsa ta farko tun bayan fara yakin Amurka da Isra’ila da Iran kusan watanni takwas da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted