Yahudawa Sun Kai Hare Hare Kan Jami’an Diflomasiyya

Yahudawa sahyoniyya sun kai hare hare kan falasdinawa fararen hula a yankin yamma da kogin Jordan, da kuma kan jami’an diblomasiyyar wasu kasashen Turai wadanda

Yahudawa sahyoniyya sun kai hare hare kan falasdinawa fararen hula a yankin yamma da kogin Jordan, da kuma kan jami’an diblomasiyyar wasu kasashen Turai wadanda suka je yankin don ganewa idanunsa irin ta’asar da HKI take yi a yankin.

Kamfanin dillancin labarann Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa yahudawan sahyoniyya yan shere wuri zaune a yankin yamma da kogin Jordan, sun kai hare hare kan falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, sannan sun farwa jami’an diblomasiyyar kasashen Faransa da magajin garin na wani birnin a kasar Faransa wadanda suke cikin kasar da aka mamaye a lokacin.

Tasnim ya kara da cewa hatta yan jarida basu tsira daga hannun yahudawan sahyoiniyya ba. Ministan harkokin wajen kasar Belguim ya bayyana cewa tare da jami’an diblomasiyyar akwai wakilan kungiyoyin kasa da kasa da dama.

Ministan harkokin wajen kasar Belgium Maxime Prevot ya kara da cewa a lokacin da yahudawa suka kai hare haren akwai babban jami’in diblomasiyya na kasarsa, a Falasdinu da jami’an diblomasiyyar Faransa da Poland da mai wakilatan cocin katolica suna da cikin wadanda yahudawan suka kaiwa hare hare a ranar asabar da ta gabata. Labarin ya bayyana cewa wasu jami’an diblomasiyya sun yi ji rauni a hareharen yahudawan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted