Gwamnatin faransa ta sanar da kafa dokar hana fita a wasu yankunan na kasar a daidai lokacin da ake fuskantar bore na jama’a kan tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi.
Haka zalika gwamnatin ta kara tsaurara matakanta ta hanyar kara zuwa ‘yan sanda, da kuma takaita taruwa.
Firaministan Faransa Sébastien Lecornu ya sanar da cewa ya nemi shugabannin kananan hukumomi da su aiwatar da dokar hana fita a matakinsu tun daga ranar Litinin da yamma, domin kare kasuwanni bayan boren karshen mako da da aka yi a fadin kasar.
Ya ambaci kaddamar da “babban matakin shari’a kan wadanda gwamnatin ta bayyana da bata gari masu samun goyan bayan wasu ‘yan adawa da rura rikicin kasar a kafin zaben shugaban kasa.
Ranar Asabar zanga zanga ta rikide zuwa tarzoma a Faransa wacce ta hada daliban makarantun sakandare, da na jami’a, ‘yan ritaya, tsoffin masu zanga-zangar Yellow Vest, da kungiyoyin kwadago, musamman babbar kunmgiyar CGT, dangane da bukatu da suka shafi wutar lantarki, hauhawar farashin makamashi da man fetur, da kuma tabarbarewar ayyukan gwamnati.
A cikin wannan yanayin, hukumomi sun kuma kara tsaurara matakai kan tarurruka.
A Marseille, wata doka ta lardin ta haramta duk wata zanga-zanga da taruka a duk fadin birnin a ranar Litinin, daga karfe 12 na rana zuwa karfe 8 na dare, a wani mataki da ta ce na hana tayar da zaune tsaye ne a bainar jama’a.”