Rundinar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi gargadin cewa, duk wani sabon hari ko ta’adi da za a kai kan Iran, za a tunkare shi da martani mai tsanani, wanda zai haifar da “babbar matsalar makamashi” a duk fadin duniya.
Kakakin rundunar IRGC, Birgediya Janar Hossein Mohebbi, ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Tehran Times, a daidai lokacin da Amurka ke kara tsananta barazanarta a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan gazawarta wajen tilasta wa kasar mika wuya.
Da aka tambaye shi game da yiwuwar sake kai hare-haren soja, ya ce Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta a yakin da ya gabata, kuma a halin yanzu ba ta da karfin da za ta iya kaddamar da sabon hari wanda zai haifar da sakamako daban da na baya.
Ya kara da cewa, yawancin sansanonin Amurka a yankin sun daina aiki, inda ya lura cewa sojojin Amurka sun gaji matuka, kuma sun janye zuwa nisan daruruwan kilomita daga Iran.
Janar Mohebbi ya ce, “Ta fuskar fasaha da aikin soja, Amurka ba ta da karfin kaddamar da sabon rikici, Sai dai, kasancewar zaben tsakiyar wa’adi na gabatowa, Amurka na iya kokarin kirkirar wasu nasarori na bogi.”
“Ba mu cire yiwuwar komai ba, kuma muna shirye don mayar da martani.
A wannan karon, martaninmu zai fi karfi sosai, Ko da matakin da Amurka za ta dauka ba shi da girma sosai, duniya za ta fuskanci babbar matsalar makamashi.”