Iran Ta Gargadi Amurka Da HKI Kan Wani Yaki A Kanta

Babban hafsan hafsanshin sojojin sojojin Iran Janar Ali Abdullahi ya fadawa Amurka da HKI kan cewa sojojinsa suna jiran su a kan duk wata wawata

manjo janar Abdullahi

Babban hafsan hafsanshin sojojin sojojin Iran Janar Ali Abdullahi ya fadawa Amurka da HKI kan cewa sojojinsa suna jiran su a kan duk wata wawata da zasu yi na fadawa kasar da Yaki. Yace idan sun yi haka zasu gamu da maida martani fiye da yakin baya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto babban kwamandan khtamul anbiya yana fadar haka a ranar Lahadi. Ya kuma kara da cewa,

Janar Abdullahi ya bayyana cewa, da alamun shugaba Trump bai da lafiya a tunaninsa, kuma mutanen Amurka suna cikin matsalolin tattalin arziki saboda wawtarsa. Ya kara da cewa Amurka da HKI sun jarraba dukkan dabarbarunsu na yaki a kan Iran ba tare da samun nasara ba. Sake jarraba abinda aka jarraba wawta ne.

Yace duk wani irin makamin da zasu yi amfani da shi a kan kasar Iran sun yi, amma a wannan karon idan sun sake wani wawtar zasu gamu da maida martani mafi tsanani kan wanda ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted