Wani babban jami’I a kungiyar Ansarullah ta kasar yamen yayi gargadin cewa duk wani hari da kasar saudiya za ta kai yamen to zai fuskanci mayar da martani mai karfi fiye da kowanne lokaci a baya, kuma ya jaddada cewa babu wasu cibiyoyin gwamnati da muhimman wurare a fadin kasar saudiya da zasu tsira daga harin.
Hizam al asad babban jami’I a bangaren siyasa na kungiyar ansarullah ya kara da cewa hari da jiragen yakin kasar saudiya suka kai kan fararen hula musamman mata da yara kanana a kasar yamen, sun faru ne a kokarin da riyad ke yi na ganin ta cimma burinta , amma duk da shekaru da ta kwashe tana ta’addanci kan kasar yamen da hadin guiwa amurka da isra’ila hakar ta bata cimma ruwa ba
Babban jami’in yayi ishara game da harin da kasar saudiya ta kai a baya bayan nan da yayi sanadiyar mutane mutane 9 da ya hada da yara biyar da mata 2 a arewa maso yammacin lardin saada a jiya lahadi, yace menene laifin yara da mata da fararen hula da za’a rika yi musu ruwan bama bamai.
Daga karshe yayi mummunan suka ga kungiyoyin kasa da kasa game da shiru da suka yi kan ci gaba da kai hare hare kan fararen hula da kasar saudiya ke yi , yace masalahar makamashi da ta kudi ce ta hana wasu kungiyoyi da dama na duniya daukar wani mataki.