China ta soki Amurka akan shiga harkokinta kasuwancinta da Iran

Kasar China ta soki Amurka kan shiga harkokinta da Iran, tare da bayyana lamarin kwace jirgin ruwan dakon kaya  da ya fito daga China zuwa

Kasar China ta soki Amurka kan shiga harkokinta da Iran, tare da bayyana lamarin kwace jirgin ruwan dakon kaya  da ya fito daga China zuwa Iran.

China ta danganta lamarin da fashin teku a game da kwace jirgin ruwan na ta.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa kasar na adawa da duk wani salon a zarge zarge marar tushe na ababen da basu dace ba.

Ya kara da cewa alakar kasuwanci ta kasa da kasa tsakanin kasashe bai kamata a rika shihigi a ciki ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Amurka, ta bude wuta kan wani jirgin dakon kaya mai lakabi da Toska a tekun Oman tare da kwace shi, inda shugaba Trump ya bayyana jirgin da cewa yana shake da kyaututukan China ga Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted