China: Dole Ne A Amince Da Ikon Iran Kan Mashigar Ruwa Ta Hurmuz

Jakadan kasar China a Tehran  ya bayyana cewa dole kasashen duniya su amince da ikon kasar Iran a kan mashigar ruwa ta Hurmuz. Kamfanin dillancin

Jakadan kasar China a Tehran  ya bayyana cewa dole kasashen duniya su amince da ikon kasar Iran a kan mashigar ruwa ta Hurmuz.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Cong Peiwu yana fadar haka a lokacinda yayi hira da shi a nan Tehran ya kuma kara da cewa, yakin da Amurka da HKI suka farwa kasar Iran baya bisa qa’ida.

Ya ce, wannan rikicin bai da mafita sai teburin tattaunawa. Ya bayyana cewa, dole ne wadan nan kasashe su mutunta yencin kasar Iran na kare kanta kuma kasar China zata ci gaba da goyon bayan Tehran. Yace kasar China bata amince da takunkuman tattalin arziki na bangare guda.

Yace Iran a matsayinta na kasa nab akin ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz, tana da hakkin kula da wannan bangaren na ruwan tekun farisa. Daga karshe yace bai kamata Amurka da HKI su farwa kasar Iran da yaki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted