Chadi : Mahamat Idriss Deby Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Da Sama Da Kashi 61%

Hukumar zaben kasar Chadi ta ayyana cewa shugaban kasar na rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Deby Itno ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka

Hukumar zaben kasar Chadi ta ayyana cewa shugaban kasar na rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Deby Itno ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da sama da kashi 61% na jimillar kuri’un da aka kada.

Shugaban Hukumar Zaben Ahmed Bartichet ya fada a ranar Alhamis cewa Deby ya samu kashi 61.3% na kuri’un, yayin da babban abokin hamayarsa kana tsohon Firaiministansam, Succes Masra, ya samu kashi 18.

Tunda farko dai babban abokin hamayyarsa Succes Masra ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mista, Masra, ya yi ikirarin samun nasara a zaben a wani sako da aka watsa kai tsaye ta shafin Facebook, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da magoya bayansa da su yi adawa da abin da ya kira yunkurin kwace zabe.

Bayanai sun ce an girke jami’an tsaro da dama a manyan tituna a babban birnin N’Djamena gabanin bayyana sakamakon zaben, saboda yadda hankula ke ta tashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments