Search
Close this search box.

Burkina Faso, Mali Da Nijar, Sun Garzaya MDD Kan Zargin Ukraine Da Ta’addanci

Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina Faso, sun kai karar Ukraine a gaban kwamitin tsaro na MDD, bisa zarginta da goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda

Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina Faso, sun kai karar Ukraine a gaban kwamitin tsaro na MDD, bisa zarginta da goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

Matakin dai na zuwa ne bayan da a kwanakin baya jami’an diflomasiyyar Ukraine suka furta wasu kalamai da kasashen uku suka ce sun nuna irin rawar da kasarsu ta taka a hare-haren da Abzinawa ‘yan tawaye suka kai wa sojojin Mali a watan jiya a yankin Tin-zawaten na kan iyaka da kasar Aljeriya inda suka kashe sojoji da dama.

A wata wasika da ministocin kasashen uku suka aike wa Kwamitin Tsaro na MDD, sun bayyana matukar kaduwarsu bisa kalaman da mai magana da yawun rundunar leken asirin Ukraine Andriy Yusov, ya yi, “na amincewa da rawar da Ukraine ta taka a hare-haren matsorata da masu aikata lafuka suka kai wa” dakarun Mali daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Yuli.

Kasashen uku Mali, Nijar da kuma Burkina, sun yi kira ga kwamitin tsaro na MDD ya dauki ”matakan da suka dace” a kan Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments