Search
Close this search box.

Borrell : Jefa Falasdinawa Cikin Yunwa Babban Laifi Ne

Babban jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, ta EU ya gargadi Isra’ila da cewa jefa falasdinawa cikin yunwa da gangan laifin yaki ne. Josep Borrell

Babban jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, ta EU ya gargadi Isra’ila da cewa jefa falasdinawa cikin yunwa da gangan laifin yaki ne.

Josep Borrell ya kuma ce dole ne gwamnatin Isra’ila ta “nisanta kanta” daga kalaman da ministanta Bezalel Smotrich ya yi.

A cikin wani sakon da ya rubuta a kan kafofin watsa labarun da kuma a cikin wata sanarwa, Borrell ya bayyana a matsayin “bayan wulakanci” wata sanarwa da ministan kudi na Isra’ila Smotrich ya yi a baya-bayan nan inda ya ce Isra’ila na iya azabtar da “fararen hula falasdinawa miliyan 2 da yunwa” har sai an sako fursunonin da aka kama a Gaza.

“Muna sa ran gwamnatin Isra’ila za ta nisanta kanta daga kalaman ministan, tare da tabbatar da gaskiya kan ayyukan azabtarwa da aka ruwaito a gidan yarin Sde Teiman,” in ji shi.

Jamus da Faransa ma sun yi Allah wadai da kalaman ministan, kuma Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun bukaci Isra’ila ta yi cikakken bincike kan zarge-zargen cin zarafi da azabtar da Falasdinawa da sojojin Isra’ila ke yi a gidajen yarinta, ciki har da cin zarafin mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments