Saudiyya Na Nazarin Kaucewa Fada Da Ansarullah Na Yemen

Kafar labaru ta Bloomberg ta ce; Saudiyya tana kokarin kaucewa fadada fada da Ansarullah na kasar Yemen bayan da Amurka ta ba ta shawarar kaucewa

Kakkabo Jirgin Saudiyya

Kafar labaru ta Bloomberg ta ce; Saudiyya tana kokarin kaucewa fadada fada da Ansarullah na kasar Yemen bayan da Amurka ta ba ta shawarar kaucewa hakan.

Majiyar ta kuma kara da cewa; Tare da cewa Saudiyya tana daura damarar yaki,amma a lokaci daya ta bude kafar tattaunawar diplomasiyya da Ansarullah ta hanyar kasar Oman.”

Amurkan dai tana jin tsoron cewa bude wani yaki zai girgizam kasuwar makamashi ta duniya.

A cikin watan Yuli ne dai sojojin Yemen su ka sanar da kakaba wa Saudiyya takunkumi ta ruwa da hana jiragenta na dakon makamashi wucewa, har sai idan Saudiyya din ta dauke wa kasar tasu takunkumin da ta kakaba mata.

Matakin na Yemen ya biyo bayan harin da Saudiyyar ta kai wa filin saukar jiragen saman a birnin San’a’a saboda ta hana jirgin saman Iran sauka.

Sojojin Yemen sun mayar da martani ta kai wa kamfanin man fetur na ” Aramco” hari da haddasa tashin gobara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted