Search
Close this search box.

Bayanin Rundunar Sojan Iran Dangane Da Ranar Jamhuriyar Musulunci

 Rundunar sojan Iran ta fitar da bayani dangane da zagayowar ranar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ake yin bikinta a kowace ranar 12 ga watan

 Rundunar sojan Iran ta fitar da bayani dangane da zagayowar ranar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ake yin bikinta a kowace ranar 12 ga watan farko na a kalandar Iraniyawa, da ya yi daidai da 31 ga watan Maris.

Wani sashe na bayanin ya kunshi cewa:

“Ranar 12 ga watan Farvardin wacce ita ce, ranar jamhuriyar musulunci ta Iran, tana cikin ranaku masu muhimmanci wajen ayyana makomar tarihin Iran wacce kuma  ta ginu akan al’umma mai tunanin juyin juya hali,basira, mumina mai tarihi.

Wannan ran ace da ta aiwatar da manufar al’umma da makomarta  a karkashin jagorancin Imam Khumaini (r.a), wacce ta hana bakin haure, su iya shimfida ikonsu akan jamhuriyar musulunci ta Iran. A karshe kuwa aka samar da tsarin demokradiyya na addini  ya hanyar kada kuri’a da kaso 98% 2 su ka amince da kafa tsarin jamhuriyar musulunci.

Bayanin ya kuma ce; Tsarin jamhuriyar musulunci na Iran sakamako ne na juyin juya hali da gwagwarmaya na shekaru masu tsawo na malaman addini da al’umma mai kishin addini, wanda aka dora shi akan ginshikin tsarin demokradiyya na addini da jagoranci na malami ma’abocin adalci wanda ya iya tafiyar da sha’anin mulki. Haka nan kuma tsari ne wanda ya ginu kan cin gashin kai na addini da ‘yanci,  wanda kuma ya zama abin koyi ne ga al’ummun duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments