Shugaba Bashar al-Assad na Siriya, ya taya zababben shugaban Iran Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben kasar.
“Ina mika sakon taya murna ta bisa amanar da al’ummar Iran masu daraja suka ba ka, ina kuma yaba wa shugabanni da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa nasarar zaben da aka gudanar, cikin kwanciyar hankali,” in ji shugaba al-Assad a cikin sakon.
Bugu da kari, ya jaddada cewa, “Al’ummar ku, masu tsayin daka a tarihi, suna da matukar muhimmanci a gare mu, yayin da muke kokarin tabbatar da kololuwar alaka.
Wannan dankon zumunci ya samo asali ne tun shekaru da dama da suka gabata na mutunta juna, da fahimtar juna, da kuma ka’idojin da ba za a taba mantawa da su ba da kasashen Siriya da Iran suka yi amfani da su.”
Shugaba al-Assad ya jaddada aniyarsa na inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Syria da Iran da kuma lalubo sabbin hanyoyin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Ya kuma tabbatar da cewa, “Hadin gwiwarmu na tsayin daka da gwagwarmaya, za ta ci gaba don kare martabar kasashenmu da kare muradun jama’armu.