Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Pakistan Da Oman

Ministan Harkokin Wajen Iran ya gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Pakistan da Oman Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta

Ministan Harkokin Wajen Iran ya gudanar da tattaunawa ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Pakistan da Oman

Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi tattaunawa daban-daban da takwarorinsa na Pakistan da kuma na Masarautar Oman.

Mataimakin Fira Minista kuma Ministan Harkokin Wajen Pakistan Mohammad Ishaq Dar ya yi magana ta wayar tarho da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasshen junansu.

A yayin kiran, ministocin harkokin waje kasashen biyu sun yi nazari kan sabbin ci gaban yankin da kuma kokarin diflomasiyya da ake ci gaba da yi, inda suka jaddada ci gaba da hadin gwiwa da shawarwari da nufin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.

A gefe guda kuma, Abbas Araqchi da Sayyid Badr Al Busaidi, ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Masarautar Oman, sun yi magana ta wayar tarho, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan sabbin ci gaban yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted