Araqchi: Babu Wani Harin Amurke Da Zai Wuce Hakan Nan Ba Tare Da Martani Mai Karfi Ba

ministan harkokin wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasar Amurka bayan harin baya bayan nan da ta kaddamar kan iran a lardin Hormuzgan cewa

ministan harkokin wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi kasar Amurka bayan harin baya bayan nan da ta kaddamar kan iran a lardin Hormuzgan cewa yana da kyau ta sani babu wani hari da zata kai da zai tafi haka nan ba tare da dakarun kare juyin na kasar sun mayar da martani ba.

yace duk da kashin da ta sha a filin daga amma har yanzu Amurka ta zabi ta gwada karfinmu , don haka ya yi gargadin cewa sojojin iran ba zu bar wani hari ko wata barazana ta wuce hakan nan ba, ba tare da daukar mataki mai kaushi ba.

yace ku fice daga yankinmu idan kona son zaman lafiya, don tarihin tekun fasha yana da shafuka masu yawa game da mummunar makoma kan duk wanda yayi kokarin yin kutse daga waje.

kafafen yada labaran kasar iran sun sanar da kai hari kan wurare daban daban a lardunan kudancin  kasar da Amurka ta kaddamar , a tsibirin Qeshem da suransu, sai dai tun kafin kai harin cibiyar bada umarni ta sojojin Amurka ta wallafa cewa ta kaddamar da hari kan kasar iran bayan harbo jirgin soji mai saukar Ungulu na Apachi da Iran tayi a kusa da gabar ruwan Oman.

sai dai tuni jami’an sojin kasar Iran ta musanta wannan zargi, kuma ta gargadi Amurka da cewa idan ta kuskura ta kai mata hari to za ta fuskanci mayar da martani mai karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted