Ministan harkokin wajen Iran wanda ya kai ziyarar aiki a kasar China domin tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu, ya ce: Iran tana kimanta matsayar kasar China akan yakin da aka shelanta, musamman yadda ta yi Allawadai da Amurka da Isra’ila.
Ministan harkokin wajen na Iran ya gana da takwaransa na kasar China Wang Yi, yana mai bayyana China a matsayin babbar abokiyar Iran, sannan ya kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu za ta kara bunkasa a halin da ake ciki.
A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ya ce; Harin da Amurka da Isra’ila su ka shelanta akan Iran ba ya bisa doka, kuma yankin yammacin Asiya ya shiga cikin yanayi na musamman,don haka da akwai bukatar a yi ganawa a tsakanin bangarorin biyu.
Haka nan kuma ya ce; Tsayar da wutar yaki baki daya, wani lamari ne da ya zama wajibi, kuma China a shirye take ta ci gaba da yin kokari domin ganin hakan ta tabbata.