Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi da Babban Daraktan Hukumar kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, a birnin Geneva, na kasar Switzerland.
A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Araghchi da Grossi sun tattauna batutuwan fasaha da suka shafi hadin gwiwar Tehran da IAEA.
Sun kuma tattauna game da tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka.
Ganawar ta zo ne a jajibirin zagaye na biyu na tattaunawar da ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Jamhuriyar Musulunci da kasar Oman ke shiga tsakani.
Grossi ya wallafa a shafinsa na ”X” cewa ya kammala “tattaunawa mai zurfi” da Araghchi, A wani bangare na tattaunawar da aka shirya yi gobe a Geneva.”
Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa Geneva a yammacin ranar Lahadi, tare da rakiyar tawagar diflomasiyya da kwararru.
Araghchi ya wallafa a shafin X cewa: “Ina Geneva don cimma yarjejeniya mai adalci…
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya riga ya sanar da cewa Mr. Araghchi zai kuma gudanar da tarurrukan diflomasiyya a gefen tattaunawar.
Amurka da Iran sun gduanar da tattaunawar farko a Oman matakin da bangarorin biyu suka bayyana da “farko ne mai kyau”.
Jerin tattaunawar sun zo ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya tura sojoji zuwa yankin, wanda hakan ke kara haddassa fargabar shiga rikicin soji.