Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Geneva na kasar Swissland don halattan taron tattaunawa da Amurka zagaye na biyu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghaei yana cewa ministan ya isa Geneva a jiya da yamma kuma ana saran a gobe talata ce bangarorin biyu zasu fara tattaunawa wanda ba kai tsaye ba, dangane da shirin nukliyar kasar ta Iran.
Labarin ya kara da cewa kamar yadda aka saba gwamnatin kasar Omman ce zata ci gaba da kai kawo tsakanin bangarorin biyu a taron na gobe.
An gudanar da zagaye na farko na taron a makon da ya gabata a birnin Mascat na kasar Omman. Kafin a ma fara tattaunawar, gwamnatin kasar Iran tace zata tattauna dangane da shirinta na makamashin Nukliya ne kawai makamanta masu linzami baya daga cikin abubuwan da za’a tattauna kansu, haka ma siyasarta a gabas ta tsakiya.
Banda haka, a cikin shirinmakamashin Nukliya za’a tattauna mizanin ko yawan makamashin Uranium wanda Iran zata tache a cikin gida ne, sannan da daukewa kasar takunkuman da suka shafi makamashin nukliya.
Ana saran Arachi zai gana da Jami’an gwamnatin kasar Swisslanda, da babban sakataren hukumar makamashin Nukliya ta duniya da kuma jawabi a taron MDD dangane da kwance damarar makaman nukliya.