Ana Zaben Cike Gurbi Na ‘Yan Majalisar Dokoki A Iran

A Iran, yau ake kada kuri’a a zaben neman cike gurbi na ‘yan majlaisar dokokin kasar, domin tantance makomar kujeru 45 da suka rage a

A Iran, yau ake kada kuri’a a zaben neman cike gurbi na ‘yan majlaisar dokokin kasar, domin tantance makomar kujeru 45 da suka rage a majalisar mai wakilai 290.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kada kuri’arsa a safiyar yau Juma’a a farkon bude rumfunan zabe zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisar dokokin zagaye na 12.

An fara kada kuri’a da misalin karfe 8 na safiyar ranar Juma’a a mazabu 22 na larduna 15.

‘Yan takara 90 ne ke fafatawa a sauran kujeru 45 na majalisar dokokin kasar a zaben fidda gwani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments