Al’ummar duniya na ci gaba da bayyana goyon bayansu ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) bayan da mai gabatar da kara na kotun, Karim Khan, ya nemi izinin bayar da sammacin kame shugabannin Isra’ila kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza duk da adawar da Amurka ta yi kan batun.
Kungiyar Tarayyar Turai tana goyon bayan kotun ta ICC “saboda muhimmiyar rawar da take takawa wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa a karkashin ikonta”, in ji kakakin kungiyar a ranar Talata bayan bukatar da mai gabatar da kara na kotun ya yi na a kamo firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan yakinsa, Yoav Gallant akan kisan kiyashin da suek jagoranta kan Falasdinawa a zirin Gaza.
Ana zargin Netanyahu da Gallant da sa ” fararen hula cikin yunwa da gangan da jagorantar hare-hare kan fararen hula” tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Ita ma Afirka ta Kudu ta yi maraba da matakin da mai shigar da kara na kotun ICC ya dauka na neman izinin fitar da sammacin kama Netanyahu da Gallant.
A wata sanarwa da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya fitar a ranar Litinin ya ce, “Dole ne a yi amfani da dokar daidai da kowa domin tabbatar da bin dokokin kasa da kasa, da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata munanan laifuka da kuma kare hakkin wadanda abin ya shafa.”
Ministan harkokin wajen kasar Denmark ya fada a ranar Talata cewa, kasar Denmark ta dauki sammacin kame kotun ICC da muhimmanci sosai.