Search
Close this search box.

An Zargi Dakarun Kai Daukin Gaggawa Da Yunkurin Kisan Gilla Kan Shugaban Gudanar Da Mulkin Sudan

An zargi Dakarun Kai Daukin Gaggawa na kasar Sudan da hannu a kokarin aiwatar da kisan gilla kan Janar Abdul-Fattah Al-Burhan  Hankalin ya karkata ne

An zargi Dakarun Kai Daukin Gaggawa na kasar Sudan da hannu a kokarin aiwatar da kisan gilla kan Janar Abdul-Fattah Al-Burhan 

Hankalin ya karkata ne ga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka shafe sama da shekara guda suna fafatawa da sojojin Sudan, bayan yunkurin kashe kwamandan sojojin kasar Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki a lokacin da yake halartar bikin yaye hafsoshi tsaro a Kwalejin Soja a yankin Jebet da ke gabashin Sudan.

Dalilin da ya sanya hakan shi ne; yadda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kwashe watanni suna amfani da jiragen saman yaki marasa matuka ciki wajen kai hare-hare musamman kan cibiyoyin soji da na tsaron kasar, wanda na karshe shi ne sa’o’i kafin harin da aka kai Jebit a lokacin da aka kai hari da jirgin maras matuki ciki kan hedkwatar hukumar leken asiri da ke yankin Kosti a kudancin kasar da ya yi sanadin mutuwar wani babban jami’i tare da jikkatan wasu na daban.

Bugu da kari, shugabannin rundunar dakarun kai daukin gaggawa, ciki har da kwamandan su, Laftanar Janar Muhammad Hamdan Dagalo, sun yi barazanar korar shugabannin sojojin da suka hada da Janar Al-Burhan da mataimakinsa Laftanar Janar Yasser Al-Atta.

Kakakin rundunar sojin Sudan Birgediya Janar Nabil Abdullah, ya kuma zargi dakarun kai daukin gaggawar da kai hari kan wani wurin biki da jirgin sama maras matuki cikilamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments