An Shirya Kai Hare-Hare Kan Sansanin Sojin Sudan Da Hedkwatar Gwamnatin Birnin Damar

An kai hari da jirage marasa matuka ciki kan sansanin sojojin Sudan da ke Rabak da kuma hedkwatar gwamnati a birnin Damar Majiyoyin soji sun

An kai hari da jirage marasa matuka ciki kan sansanin sojojin Sudan da ke Rabak da kuma hedkwatar gwamnati a birnin Damar

Majiyoyin soji sun ruwaito wa tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Wani jirgin sama maras matuki ciki ya yi nufin kai hari kan sansanin sojoji a birnin Rabak, babban birnin jihar White Nile na kasar Sudan, kuma sojojin sun samu nasarar kakkabo jirgin don haka bai cimma nasarar kaiharin kan sansanin sojojin ba.

Majiyoyin cikin gida sun shaidawa tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Wasu jirage marasa matuka ciki guda biyu sun tunkari kan hedkwatar gwamnati a birnin Al-Damer na jihar kogin Nilu da ke arewacin kasar, da kuma sansanin sojoji na birnin Rabak da nufin kai musu hare-haren wuce gona da iri, inda daya daga cikin jiragen ya nufi ginin ma’aikatar kananan hukumomi da ke arewacin babban birnin kasar, Khartoum kuma ginin ya kama wuta, yayin da dayan ya fado kusa da sakatariyar gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments