An Raya Daren Farko Na Dararen “Lailatul-Qadari” A Iran

A jiya Juma’a ne al’ummar Iran su ka raya daren farko daga cikin dararen ‘lailatul-Qadari’ a cikin masallatai da wasu cibiyoyi na addini ta hanyar

A jiya Juma’a ne al’ummar Iran su ka raya daren farko daga cikin dararen ‘lailatul-Qadari’ a cikin masallatai da wasu cibiyoyi na addini ta hanyar  karatun alkur’ani da yin adduo’i.

Da asubahin ranar 19 ga watan Ramadan ne dai wani Bakawarije, Ibn Muljim ya sari Imam Ali (a.s) da takobi a lokacin da ya yi sujjada yana limancin sallar asuba a masallacin Kufah. Takobin Ibn Muljim wacce take da guba ta yi wa Imam Ali raunin da shi ne ya yi sanadiyyar shahadarsa a ranar 21 ga watan Ramadan.

Mabiya mazhabar Ahlul Bayti ( a.s) a duniya suna raya wadannan dararen na 19, 21 da 23 ga watan Ramadan ne da karatun alkur’ani da kuma addu’oi da zummar neman gafara a wurin Ubangiji madaukakin sarki.

Daga cikin muhimman cibiyoyin da aka yi wadanan addu’oin da akwai Haramin Imam Ridha (a.s) a Mashhad, da na Fatimah Ma’asumah dake birnin Kum da wasu daruruwan cibiyoyin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments