An mika ma’aikatan jirgin ruwan Iran da Amurka ta kwace ga Pakistan

Bayanai sun ce an mika ma’aikatan jirgin ruwan kasuwanci na Iran Touska, wanda Amurka ta kwace a matsayin wani bangare na toshewar jiragen ruwanta ba

Bayanai sun ce an mika ma’aikatan jirgin ruwan kasuwanci na Iran Touska, wanda Amurka ta kwace a matsayin wani bangare na toshewar jiragen ruwanta ba bisa ka’ida ba, inda ka mika su ga Pakistan sannan su wuce zuwa Iran.

Cibiyar sadarwa ta Amurka ta kara da cewa, an saukake shirye-shiryen mika ma’aikatan jirgin su 22.

Bugu da kari, rahoton ya bayyana cewa an fara aiwatar da matakan mayar da jirgin ruwan ga mai shi.

An kwace jirgin a watan da ya gabata.

Amurka ta sanar da sanya takunkumin a ranar 13 ga Afrilu sannan ta ba da umarnin ci gaba da shi, duk da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu da Pakistan ta shiga tsakani kuma Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar, da nufin kawo karshen yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran ba tare da wani dalili ba.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da toshe tashohin jiragen ruwan ta.

Tehran ta kuma bayyana kwace jiragen ruwan a matsayin ” fashin teku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted