An Kasa Cimma Matsaya A Tattaunawa Da Aka Yi Kan Makomar Yankin Greenland

Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar da aka tsakanin manyan jami’ai game da makomar Greenland an kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba, bayan da

Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar da aka tsakanin manyan jami’ai game da makomar Greenland an kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba, bayan da shugaban Amurka Donald trump ya nuna bukatar kwace ikon kula da yankin, da hakan ya kara tada zaman tankiya tsakaninsa da kawayensa na kasashen turai.

Taron ya gudana ne a birnin Washington  da ya hada da mataimakin shugaban Amurka JD vence da sakataren harkokin cikin gida Marco Rubio da kuma ministan harkokin wajen Denmark lars Rasmussen da kuma ministan harkokin waje na Greenland Vivian Motzfeldt sai dai an tashi baran-baran ba tare da cimma wata matsaya ba.

Trump ya kara da cewa Greenland yana da muhimmanci sosai ga tsaron kasa har da ma kasar Denmark, yace matsalar itace babu abin da Denmark za ta iya yi idan rasha ko china suna son mamaye Greenland amma akwai abin da zamu iya yi kuna fahimci haka a makon jiya kan yadda muka yi da Venzuwela

Tuni kasashen Sweden, faransa, Norway suka fara aikewa da dakarunsu zuwa yankin na Greenland kamar yadda kasar Denmark ta bukacesu, itama tana ci gaba da aikewa da jiragen yaki da sojoji a wani bangare nan a ganin sun karfafa samuwar kungiyar tsaro ta Nato a wajen.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments