Mededov Na Rasha: Cikin Sauki Kasashen Turai Za Su Mika Wa Amurka Yankin Greenland

Shugaban  Majalisar tsaron kasar Rasha Dmitry Mededov ya ce; Duk da cika bakin da kasashen turai suke yi akan batun Greenland, sai dai abu ne mai yiyuwa su mika yankin ga Amurka acikin sauki. Demitry Mededov wanda yake mayar da martani akan furucin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron akan cewa idan aka  keta hurumin kasar […]

Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Za Ta Janye Daga Yankin Gaza Ba

A daidai lokacin da ake batun shiga mataki na biyu a yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun ce, ba za su janye ba  daga wuraren da su ka shiga ba a cikin zirin Gaza. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa a daidai lokacin da ake Shirin shiga mataki na gaba a […]

Kasar Sudan Ta Koka Kan Yankewar Dukkanin Hanyoyin Samun Kudaden Shigarta

Gwamnatin Sudan ta sanar da yankewar dukkanin hanyoyin samun kudaden shigarta tun bayan fara yakin basasar kasar a watan Afrilun shekara ta 2023 tsakanin dakarun kasar da mayakan RSF wanda yanzu haka ke cika shekaru 3 cif da farawa. Ministan kula da harkokin kudade na kasar Gibril Ibrahim da yake sanar da hakan ga kamfanin […]

An Karawa Malaman Jamai’oi Albashi Kashi 40%  A nageriya A sabuwar Yarjejeniya

Bayan kwashe shekaru 16 ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’oi ta Asuu daga karshe dai gwamnati ta amince da karin albashi kashi 40% ga dukkan malaman jami’oi a jamioin gwamnati dake fadin kasar, bayan yarjejeniyar da aka sanyawa hannu tsakanin gwamnti da Asuu. Ministan ilimi na kasa Dr Tunji alausa shi ne […]

An Kasa Cimma Matsaya A Tattaunawa Da Aka Yi Kan Makomar Yankin Greenland

Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar da aka tsakanin manyan jami’ai game da makomar Greenland an kawo karshe ba tare da cimma matsaya ba, bayan da shugaban Amurka Donald trump ya nuna bukatar kwace ikon kula da yankin, da hakan ya kara tada zaman tankiya tsakaninsa da kawayensa na kasashen turai. Taron ya gudana ne a […]

Iran Ta Gargadi Trump Kan Kokarin Isra’ila Na Jefa Amurka Cikin Yaki A Madadinta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi gargadi shugaban Amurka Donald Trump game da kokarin Isra’ila na yin amfani da shi wajen jefa Amurka cikin yakin soji kai tsaye da kasar Iran a madadinta. Acikin shafinsa na X ministan ya bayyana irin tarihin dabarun halayen gwamnatin sahyuniya na kokarin cimma manufofinta ta hanyar […]

Araghchi : Mun samu shawo kan tarzomar da ta barke

Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi Ya Danganta tarzomar da ta barke a kasar kwanan Nan da Wani makircin Isra’ila don tada hankali da kuma niyyar kai sabon hari kan Jamhuriyar Musulunci. Babban jami’in diflomasiyyar ya yi wannan tsokaci ne a wata hira ta musamman da tashar talabijin ta Amurka Fox News. Da yake mayar da […]

Iran ta danganta Sabbin takunkuman Amurka a matsayin take hakkin bil’adama

Iran ta bayyana sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata a matsayin take hakkin bil adama. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Esmail Baqai, ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman kan tattalin arziki da Amurka ta sanya wa abokan huldar Iran a ranar Laraba. ” Da yake fassara matakan Amurka na baya-bayan nan a matsayin ci […]

Ana zaben Shugaban kasa a Uganda

A Uganda yau ne al’ummar kasar ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar. Masujefa kuri’a miliyan 21.6 ne aka kira zuwa rumfunan zabe a fadin kasar. Shugaba mai ci Yoweri Museveni, wanda ya hau mulki a watan Janairun 1986, wato sama da shekaru arba’in da suka gabata, yana neman wa’adi na bakwai a kan ‘yan […]

Amurka ta soke bada biza ga ‘yan kasashe 75, ciki har da na Afirka 26  

Amurka ta sanar da dage aiwatar da bada takardar izinin shiga kasar ga ‘yan kasashe 75, ciki har da kasashen Afirka 26. Wannan shawara wani bangare ne na tsaurara manufofin shige da fice da Donald Trump ya fara tun bayan komawarsa mulki. Wadannan takardun izinin shiga sun shafi mutanen da ke neman zama na dindindin […]

Morocco da Senegal zasu kara a wasan karshe na Afcon

Morocco ta doke Najeriya 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida Sai Senegal wacce ta lallasa Masar da 1-0 Ran Asabar za a fafata tsakanin Masar da Najeriya domin neman matsayi na uku. Yayin da Morocco mai masaukin baki zata kece raini da Senegal a wasan karshe na gasar a ranar Lahadi