An Kafa Sabuwar Majalisar Ministoci A Kasar Afirka Ta Kudu

Jam’iyyar African National Congress, wadda take mulki a ƙasar tun 1994, ta samu ministoci 20 daga cikin 32, waɗanda suka haɗa da ministocin harkokin waje,

Jam’iyyar African National Congress, wadda take mulki a ƙasar tun 1994, ta samu ministoci 20 daga cikin 32, waɗanda suka haɗa da ministocin harkokin waje, da kuɗi da tsaro, da shari’a da ‘yan sanda.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ƙaddamar da gwamnatinsa ta haɗaka ranar Lahadi inda ‘yan adawa suka samu ministoci 12 cikin 32 bayan sun haɗa gwiwa wajen lashe zaɓen ‘yan majalaisar dokokin da aka gudanar a watan jiya saboda jam’iyyar ANC ta gaza yin nasarar da ake buƙata a zaɓen kai-tsaye.

Jam’iyyar African National Congress, wadda take mulki a ƙasar tun 1994, ta samu ministoci 20 daga cikin 32, waɗanda suka haɗa da ministocin harkokin waje, da kuɗi da tsaro, da shari’a da ‘yan sanda.

Babbar jam’iyyar da ta shiga gwamnatin haɗakar, Democratic Alliance (DA), za ta samu ministoci shida da suka haɗa da ministan harkokin cikin gida da muhalli da ayyuka.

An naɗa shugaban jam’iyyar DA John Steenhuisen, mai shekaru 48, a matsayin Ministan Harkokin Noma.

Jam’iyyar Inkatha Freedom Party (IFP) mai kishin al’ummar Zulu da sauran ƙananan jam’iyyu sun samu ministoci shida, waɗanda suka haɗa da ministan gyaran hali da sauye-sauye kan dokokin mallakar ƙasa da wasanni da yawon buɗe ido.

Yayin da yake jawabi a gidan talbijin bayan ƙaddamar da sabuwar majalisar ministocin, Shugaba Ramaphosa ya ce, “ba a taɓa kafa gwamnatin haɗaka a tarihin dimokuraɗiyyarmu ba”.

Ya ƙara da cewa “wannan gwamnati za ta mayar da hankali cikin gaggawa wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ƙarin adalci a cikin al’umma.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments