An Gano Gawarwakin Falasdinwa 112 Da Isra’ila Ta Kashe A Gaza

Kungiyar Gwagwarmaya ta Hamas ta bayyana cewa gano gawarwakin falasdinawa 112 karkashin burabusten gine-gine bayan kusan shekaru 3 da hare-haren da isra’ila ta kai yana

Kungiyar Gwagwarmaya ta Hamas ta bayyana cewa gano gawarwakin falasdinawa 112 karkashin burabusten gine-gine bayan kusan shekaru 3 da hare-haren da isra’ila ta kai yana kara tabbatar da irin laifukan yaki da ta tafka kan alummar falasdinu a lokacin yaki

Khalil Al-Hayya shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas ya mika ta’aziyya ga iyalan Abu sharia da kuma iyalan Al-hasaynah  bayan bizne gawarwakin yan uwansu guda 112 da aka gano karkashin burabutsen gine-gine a yankin Sabra dake makwabtaka da yankin Gaza, inda suka samu mafaka daga hare-haren isra’ila kafin ta tarwasta gini.

Al-hayya ya bayyana abin da ya faru a matsayin daya daga cikin mummunan kisan gilla da isa’ila ta yi  a yakin kare dangi da ta kaddama a gaza, gawarwakin wadanda abin ya shafa sun ci gaba da kasancewa karkashin burabutsai  kusan shekaru 3 kafin a gano. don haka jinin wadannan shaidai zai ci gaba da zama a matsayin sheda rayayye na irin laifukan yaki da Isra’ila ta aikata, yace kuma mafi yawanci gawarwakin na mata da yare kanana ne .

A lokacin jana’izar kakakin dakarun sa kai a yankin gaza Mahmud basal ya yi kira ga majalisar dinkin duniya inda ya tambayesu me yasa ake ci gaba da kashe yara kanana a yankin Gaza , kuma ya bukaci alummar duniya da su dauki matakin da ya dace kan irin mawuyacin hali da alummar falasdinu suke ciki

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted