Search
Close this search box.

An fitar da rahoto kan adadin rayukan da suka salwanta a Najeriya a cikin shekaru 5

Kungiyar Global Rights a Najeriya ta ce a cikin shekaru 5 da suka gabata, ƴan bindiga sun kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 24

Kungiyar Global Rights a Najeriya ta ce a cikin shekaru 5 da suka gabata, ƴan bindiga sun kashe mutanen da yawansu ya kai dubu 24 da ɗari 8 da 16, yayin da kuma suka yi garkuwa da wasu mutum dubu 15 da 597, wanda ke da nasaba da sake taɓarɓarewar harkokin tsaro a ƙasar.

Global Rights ta bayyana cewa cikin wannan adadi na mutum kusan dubu 25 da ‘yan bindigar suka kashe a Najeriya har da manoma dubu 1 da 356 galibinsu daga yankin arewacin Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2024.

A cewar ƙungiyar wannan matsalar ta ruɓanya tsakanin watan Yulin shekarar 2023 zuwa Yunin shekarar 2024.

Kungiyar Global Rights ta ce matsalar ta fi kamari a yankin arewacin Najeriya, mai fama da matsalolin tsaro.

A cewar Global Rights aƙalla mutane miliyan 3 da dubu 400 yanzu haka suka gujewa muhallinsu da garuruwansu saboda wannan tashin hankalin.

Daraktar kungiyar ta Global Rights a Najeriya Abiodun Bayeiwu ta ce akwai ‘yan Najeriya sama da dubu 100 da yanzu haka ke gudun hijira a ƙasashen maƙwabtaka.

Bayeiwu ta kara da cewar a yankin arewacin Najeriya akwai akalla mutane dubu 457 da tashe tashen hankula suka tilastawa barin muhallinsu, adadin da ya ribanya na shekarar 2022 da ƙasar ta gani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments