Mahukuntan Saudiyya sun kulla yarjejeniyar shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da kasar Yemen
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Yemen da Saudiyya ta samu karbuwa sosai a sassan kasar Yemen, yayin da yarjejeniyar tafi mai da hankali kan magance matsalolin da suka shafi batun jin kai da tattalin arziki, musamman soke matakan neman gurgunta ayyukan bankunan kasar Yemen, da dawo da zirga-zirgar jiragen sama na Yemen tsakanin Yemen da Jordan, da bude kofa ga kasashen waje ciki har da sabbin kamfanonin jiragen sama da zasu din ga safara zuwa kasashen Masar da Indiya.
Al’ummun kasashen biyu da mahukuntansu sun yi maraba da cimma wannan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu, don magance batutuwan da suka shafi jin kai da tattalin arziki, abin da ya fi daukar hankali shi ne soke shawarar daukan matakan da gwamnatocin kasashe ‘yan amshin shatan Saudiyya suka dauka a baya-bayan nan kan bankunan kasar Yemen da nufin rusa harkokin tattalin arzikin kasar. Baya ga matakin sake dawo da zirga-zirgar jiragen sama na filin jirgin saman birnin Sana’a.
Masu lura da al’amura na ganin cewa: Saudiyya ta janye daga kan matakan da ta dauka na baya-bayan nan kan kasar Yemen ne, saboda kaucewa munanan matakan mayar da martani da take fuskanta daga al’ummar Yemen.
Mai ba da shawara ga majalisar koli ta harkokin siyasar Yemen Muhammad Muftah ya ce: Cimma yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu, wani abin takaici ne ga gwamnatin Amurka da kuma yahudawan sahayoniyya da suke son wurga gwamnatin Saudiyya cikin rikici da al’ummar Yemen domin ta ci gaba da yaki da Yemen a maimakonsu.