A wani sako na sirri da kwamandan sojan Amurka a nahiyar turai Alexus Gregory Grynkewich ya aike wa “Pantagon” yana mai cewa; Kayan aiki da suke da su, ba su wadatar ba da za su ci gaba da bai wa “Isra’ila” kariya daga makaman Iran masu linzami.
Jaridar Washington Post ta buga labarin da yake cewa; Idan har ba a sake tura masa wani jirgin yaki ba, to ba shi da zabi, sai ya bai wa Amurka kariya maimakon Isra’ila.”
A gefe daya wani dan majalisar Amurka mai wakiltar jam’iyyar “Republican”ya bayyana cewa; suna cikin damuwa akan raguwar da makamansu na kare sararin samaniya suke karewa.
Dan majalisa Rick Crawford ya fada wa tashar talabijin din “Fox News” cewa; Muna cikin damuwa akan yiyuwar karewar makamanmu na kariyar sararin samaniya, idan har fada da Iran ya ci gaba.
Dan majalisar na Amurka ya yi kira ga shugaba Donald Trump da ya kawo karshen yaki da Iran.