Amurka Ta Gargadi Babban Lauya Mai Shigar Da Kara A Kotun Kasa Da Kasa

Amurka ta yi barazana ga babban lauya mai shigar da kara a kotun kasa da kasa ta ICC cewa zai fuskanci mayar da martani, idan

Amurka ta yi barazana ga babban lauya mai shigar da kara a kotun kasa da kasa ta ICC cewa zai fuskanci mayar da martani, idan har ya fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila

Mambobin majalisar dattijan Amurka sun yi barazana ga mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Karim Khan da sauran ma’aikatan kotun da iyalansu, idan Khan ya fitar da sammacin neman kama fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan yakin yahudawan sahayoniyya Yoav Galant da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Herzi Halevy, kan zargin muggan laifukan yaki da sojojin yahudawan sahayoniyya suka aikata a Zirin Gaza da suka hada da wurga al’ummar cikin kangin yunwa, to lallai zai fuskanci mayar da martani mai gauni. Shafin yanar gizo na Amurka “Axios” ya ruwaito cewa: Sanatocin jam’iyyar Republican 12 ne suka aike da wasikar barazanar ga Karim Khan, suna gargadinsa cewa: Idan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC ta yi gigin fitar sammacin neman kama Netanyahu da manyan jami’ansa kan zargin tafka laifukan yaki a Zirin Gaza, to zai ga

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments