Jami’an leken Amurka sun nuna damuwa game da “barazanar leken asiri” da Isra’ila ke fuskanta yayin da Washington ke tattaunawa da Iran, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito.
Wasu jami’an Amurka sun yi imanin cewa kokarin da Isra’ila ke yi na tattara bayanai kan matsayin Amurka a tattaunawar Iran ya “ketare iyaka,” in ji jaridar.
Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta kara sa ido kan manyan jami’an Amurka, ciki har da babban mai shiga tsakani na Shugaba Donald Trump Steve Witkoff, da shugaban manufofin Pentagon Elbridge A. Colby da mataimakinsa, Michael P. DiMino IV.
Wani rahoto na daban na Hukumar Leken asiri ta Tsaro ya daga matakin barazanar leken asiri na Isra’ila daga “babba” zuwa kololuwa,” yana ambaton kokarin leken asiri kan ma’aikatan sojan Amurka da jami’an gwamnati.
Damuwar ta zo ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke hadin gwiwa a yakin da suke yi da Iran.
Koda yake Amurka tana raba manyan bayanan sirri na dabaru da aiki tare da Isra’ila, jami’an Amurka sun yi imanin cewa Isra’ila tana neman zurfafa fahimtar dabarun tattaunawar Trump da kuma matsayin da ke tasowa kan tattaunawar.
Jaridar ta ce gargadin zai iya kara dagula hadin gwiwar sojoji idan Pentagon ta matsa lamba don takaita raba bayanai da jami’an Isra’ila.