Yakin da Amurka ke jagoranta kan kasar Yemen domin kare muradun Isra’ila a tekun Bahar Rum na fuskantar gagarumar matsala mafi tsanani tun bayan yakin duniya na biyu, kamar yadda wani rahoton AP da ya ambato kwamandojin sojin Amurka da kwararru suna fadar hakan.
Rahoton ya ce sojojin ruwan Amurka sun nuna gajiyawa bayan sun yi arangama da hare-haren wuce gona da iri da sojojin Yaman suka yi sama da watanni bakwai, inda kwamandojin suka yi gargadin cewa halin da ake ciki na da matukar hadari a gare su.
Bryan Clark, wani tsohon sojan ruwa ne kuma babban jami’i a Cibiyar Hudson, ya shaida wa AP, “wannan shi ne yaki mafi muni da sojojin ruwan Amurka suka gani tun yakin duniya na biyu.”
“Muna kan hanyar da Houthis za su iya kai nau’ikan hare-haren da Amurka ba za ta iya dakatar da su a kowane lokaci ba, sannan za mu fara ganin barna mai yawa. Idan kun bar lamarin ya ta’azzara, Houthis za su kasance masu iya aiki, da kai hare-hare da kwarewa ” in ji shi.