A Amurka an fara aza ayar tambaya game da batun tsaro ga mayan jami’an tsaron kasar bayan harin da wani dan bindiga ya kai a wajen liyafa da ‘yan jarida a birnin Washigton.
An kai harin ne a wajen liyafar cin abincin dare na shekara-shekara na kungiyar ‘Yan Jarida ta Fadar White House a Otel din Hilton da ke Washington.
Donald Trump ya halarci taron tare da Uwargidansa da Mataimakiyar Shugaban Kasa JD Vance, da wasu manyan jami’an Amurka da dama.
Saidai an katse taron, ba zato ba tsammani bayan an ji karar harbe-harbe kusa da babban zauren.
Hukumomi ba su tabbatar da asalin maharin ba tukuna, amma a cewar kafofin watsa labarai na Amurka, ciki har da jaridar New York Times, mutumin mai shekaru 31 mai suna Cole Tomas Allen malamin makaranta daga California.
Bayan lamarin, Donald Trump ya bayyana cewa ginin “ba shi da tsaro sosai.”
Da farko shugaban ya so ya ci gaba da taron, kafin a yanke shawara kan soke shi saboda dalilai na tsaro. Sannan ya na yiwuwar sake tsara liyafar cin abincin dare.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da badakalar siyasa da suka shafi makusantan Trump.
A shekarar 2024, Donald Trump ya ji rauni a wani yunkurin kishe shi a Pennsylvania, kafin kuma a dakile wani yunkurin ‘yan makonni a Florida.