Rahotonni sun bayyana cewa: An shirya wata gagarumar zanga-zanga a kasar Tunusiya a jiya Lahadi, a gaban ofishin jakadancin Amurka, domin nuna goyon baya ga al’ummar Gaza da kuma yin tofin Allah tsine kan zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummar Falasdinu, da kuma neman korar jakadan Amurka tare da rufe ofishin jakadancinta a kasar saboda tallafawa da take yi a ayyukan ta’addancin yahudawan sahayoniyya.
Al’ummar kasar Tunusiya dai na ci gaba da gudanar da jerin gwano tun daga lokacin da yahudawan sahyoniyawan suka fara gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga zirin Gaza, domin nuna goyon bayansu ga tsayin daka da kuma neman kawo karshen laifukan kisan kiyashi da ake yi a Gaza a hannun haramtacciyar kasar Isra’ila.
Shugaban kungiyar hadin kan kasar Tunusiya Salahuddin al-Masry a cikin wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila za ta ruguza kanta idan har ta kuskura ta yi gigin fuskantar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon, kamar yadda Amurka ta aike da sako zuwa ga yahudawan sahayoniyya da su nisanci kaddamar da yaki kan Lebanon. Sannan shugaban kungiyar ya yaba da matsayin kasar Yemen, wanda ya kaskantar da sojojin yahudawan sahayoniyya da Amurka.