A cikin yankuna da dama na Iran al’ummar kasar sun fito kan tituna domin yin murna akan martanin da Iran ta mayarwa HKI
Al’ummar Iran da su ka yi gangami a muhimman wuraren taruka,sun rika bayar da taken nuna farin cikinsu akan harin da kuma yin tir da HKI.
Wannan harin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Iran dake birnin Damascuss na kasar Syria.