Shugaban majalisar shugabancin kasar Yemen Mahdi Almashat ya bayyana cewa, yahudawan sahyuniya su dakaci daukar fansa daga al’ummar Yemen kan shahahar kami’ansu da Isra’ila ta kaiwa hari.
Ya ce tabbas Faraminista da sauran jami’ai ministoci da sua yi shahada sun yi sadaukarwa ne a kan tafarkin taimakon al’ummar Falastinu, kuma a kan wannan tafarki ne suka yi shahada
Ya kuma jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen ci gaba da daukar dukkanin matakai na kara matsi a kan yahudawa domin kawo karshen kisan kiyashi a Gaza.