Aljeriya: Ba za mu amince da duk wani katsalandan daga waje a harkokin Libya ba

Gwamnatin kasar Aljeriya ta jaddada muhimmancin cimma sulhu a kasar Libya tare da halartar dukkan bangarorin kasar Libya, a cikin tsarin cikakken aikin kasa da

Gwamnatin kasar Aljeriya ta jaddada muhimmancin cimma sulhu a kasar Libya tare da halartar dukkan bangarorin kasar Libya, a cikin tsarin cikakken aikin kasa da ya cika halastattun burinsu na kafa kasa mai bin tsarin demokradiyya.

Libya dai ta fada cikin dambarwa da rarrabuwar kawuna da tashe-tashen hankula ne tun bayan harin da kungiyar tsaro ta NATO ta kai a kasar a shekara ta 2011, inda ta hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi.

Kasar mai arzikin makamashi ta rabu ne tsakanin gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita mai mazauni a babban birnin kasar Tripoli a yammacin kasar, da kuma gwamnatin adawa da ke mulki daga Benghazi da Tobruk a gabas.

An shirya gudanar da zaben shugaban kasa da nufin hada kan kasar da ta tabarbare a karshen shekarar 2021 amma har inda ya take ba a iya ggudanar da zaben ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments